Ƴan wasan Real da za su kara da na Atletico a La Liga


 Real Madrid za ta karɓi bakuncin Atletico Madrid a gasar La Liga karawar mako na 23 da za su fafata a wasan hamayya ranar Asabar a Santiago Bernabeu.

Wannan shi ne karo na biyu da su kece raini a tsakaninsu a bana, sun tashi 1-1 a Atletico a babbar gasar tamaual ta Sifaniya ranar Lahadi 29 ga watan Satumba.

Wannan shi ne karon farko da za su fuskanci juna a wasan na ƴan birnin Madrid a 2025.

Real Madrid ce kan gaba a teburin La Liga da tazarar maki ɗaya tsakani da Atletico ta biyu mai maki 48.

Kociyan Real Madrid, Carlo Ancelotti na fatan magoya baya za su mara musu baya tun daga take leda zuwa tashi, domin su samu maki ukun da suke bukata.

Real za ta fuskanci Atletico Madrid, bayan kai wa zagayen daf da karshe a Copa del Rey, sakamakon doke Leganes a Butarque.

Haka kuma za ta yi karawar da ƙwarin gwiwa, bayan da Camavinga ya warke, haka kuma Jude Bellingham da Kylian Mbappe da ba su buga Copa del Rey, za su fuskanci Atletico.

Mbappe ƙyaftin ɗin tawagar Faransa ya ci wa Real ƙwallo 22 a dukkan karawa, kuma wasan hamayya na farko da zai yi da Atletico Madrid.

Atletico Madrid dai ba kanwar lasa bace, domin itama ta kai zagayen daf da karshe a Copa del Rey.

Haka kuma ita ce ta biyu a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya, wadda ta ci wasa 14 da canjaras shida aka doke ta karawa biyu.

Griezmann da Sorloth sune kan gaba a ci wa ƙungiyar ƙwallaye a La Liga a kakar nan, kowanne ya zura takwas a raga.

Ƴan wasan Real da za su kara da Atletico:

Masu tsare raga: Courtois, Lunin, Sergio Mestre.

Masu tsare baya: Lucas Vázquez, Vallejo, Fran García, Mendy, Jacobo, Asencio, Lorenzo.

Masu buga tsakiya: Bellingham, Camavinga, Valverde, Modrić, Tchouameni, Arda Güler, Ceballos.

Masu cin ƙwallaye: Vini Jr., Mbappé, Rodrygo, Endrick, Brahim, Gonzalo.

Comments

Popular Posts