Neymar ya raba-gari da Al-Hilal


 Neymar ya tafi Al-Hilal ne kan kuɗi Yuro miliyan 90 (fam miliyan 77.6) a 2023

Sa'o'i 7 da suka wuce

Ƙungiyar Al-Hilal ta Saudiyya da ɗan wasan Brazil Neymar sun amince su kawo ƙarshen kwantaragin ɗan wasan.


Neymar, mai shekara 32 a duniya ɗan asalin ƙasar Brazil ya je Al-Hilal ne a watan Agustan shekarar 2023 kan kuɗi Yuro miliyan 90, sai dai sau bakwai kacal ya buga wa ƙungiyar wasa sanadiyyar rauni da ya addabe shi.


A kakar da ke ci sau biyu kawai Neymar ya buga wasa, na baya-bayan shi ne lokacin da aka yi canji da shi a watan Nuwamba.


Ana alaƙanta shi da komawa ƙungiyarsa ta asali, wato Santos, da ke Brazil.


"Ƙungiyar ta gode wa Neymar kan gudumawar da ya bayar a lokacin zaman shi a Al-Hilal, kuma tana masa fatan alkhairi a nan gaba," in ji ƙungiyar.

Comments

Popular Posts