Abin da ya sa birnin Goma ke da muhimmanci ga ƴan tawayen M23


 

  • Marubuci
  • Sanya sunan wanda ya rubuta


  • Sa'o'i 6 da suka wuce

  • Birnin Goma da ke gabashin Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo da ya kwashe gwamman shekaru yana fama da fada a lokuta mabambamta, ya sake zama cibiyar yaki tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawayen M23.

  • Yaki tsakanin bangarorin biyu ya munana a farkon shekarar nan, hakan ya tilasta wa farar hula sama da 400,000 tserewa daga muhallansu a cikin shekarar nan kawai.

  • Shin wane muhimmanci birnin na Goma ke da shi a ƙasar?

  • Su wanene ƴan tawayen M23?

  • Sama da shekara 10 ke nan da kungiyar masu dauke da makamai ta M23 suka balle daga cikin sojojin gwamnatin Congo, kan ikirarin bai wa 'yan kabilar Tutsi kariya wanda suka jima su na korafi akansu, wajen nuna musu wariya da yanke musu hukuncin zalunci.


  • Majalisar Dinkin Duniya ta ce gwamnatin Rwanda da ke makoftaka, na bai wa 'yan tawayen M23 kariya, amma Rwanda ta musanta hakan.

  • A baya-bayan nan Rwanda ta ce hukumomi a Congo na aiki tare da wadanda suka kitsa kisan kare dangin da kabilar Hutu suka yi wa kabilar Tutsi a Rwanda a shekarar 1994,

  • A shekarar 2012, 'yan tawayen sun mamaye birnin Goma na kwanaki 10, kafin daga bisani su fice daga ciki bayan matsin lambar kasashen waje.

  • Wannan ya janyo 'yan tawayen M23, su ka sha akaye aka ci su da yaki wanda dole suka tsere suka bar sojojin Congo da dakarun wanzar da zaman lafiya da yin nasara.

  • Daga nan mayakan M23 su ka amince su koma cikin rundunar sojin kasar kan alkawarin za a bai wa kabilar Tutsi dukkan kariyar da suke bukata.

  • Sai dai a shekarar 2021, lamura suka sauya inda 'yan tawayen suka sake daukar makamai, suka fake da cewar an karya alkawarin da ke tsakaninsu da sojin gwamnatin Congo.

  • Tun daga wannan lokacin 'yan tawayen M23, ke ci gaba da mamaya da karbe iko da yankuna, da kauyuka d garuruwa daban-daban na kasar. Kwararru a MDD sun ce sojojin Rwanda 4,000 ne ke taimakawa 'yan tawayen M23 a yammacin Congo.

Comments

Popular Posts